Labarai

Soayyar Facebook tazo Abuja don ta hadu da Saurayi shi Kuma ya kashe wayarsa.

Spread the love

Wani Saurayi yaƙi yarda ya haɗu da Budurwar sa ƴar Shekaru 25 Da suka haɗu A Facebook wadda ta taho daga Legas zuwa Abuja Dan ta Ganshi.

Wata mai shekaru 25 mai suna Sandra ta makale a yankin Kubwa da ke Abuja duk da dai ta samu taimakon mutane da ke kusa da yankin na Abinci da kuɗin mota.

Budurwar Ta bayar da labarin yadda ta hadu da Saurayinta a shafin Facebook a ranar masoya kuma tayi alkawarin ziyartar sa a Abuja daga jihar Legas.

Bayan isar ta Abuja ne sai ta riƙa kiran sa tana jin lambar a kashe alhali tun tana hanya suke waya tana ce masa muna wuri kaza mun zo gari kaza, inji ta.

Da farko dai, mutumin da aka ambata da suna D-Boy ya yi wa matar alkawarin cewa zai biyata duk kudin motar da ta kashe in har ta iso wajen sa daga legas zuwa Abuja.

Mutane sun fara caccakar budurwar saboda zuwanta daga Legas don haduwa da wani mutum da ba ta sanshi ba sai a Facebook, kazalika sun ce muna ba sauran matasa mata shawara da suyi koyi da labarin Sandra mai shekaru 25 kuma su kiyaye.

Me zaku ce?

Daga Dimokuraɗiyya Adon ƙasa!

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button