Social Distancing Ko Rainin Wayo Da Fada Da Addini?
Daga Kais Dauda Sallau
Wai a hakan za a zo Kaduna ana yi mana muzurai, ana rufe mana gurin Ibadunmu da kasuwanninmu.
Wani wai social distancing, social distancing ko renin wayo da faɗa a addini.
Za ku yi taron ku na siyasa ba social distancing wadansun ku ma ba face mask, masallatai mu da coci an rufe, an hana mu yin Ibadunmu a ciki wai sai Jumma’a da Lahadi kuma wai a yi wata shegiya social distancing. An rufe mana kasuwanni, an hana mutane su je su nima abinda da za su riƙe kan su na yau da gobe. An rufe makarantu yaran mu suna zaune a gida ba karatu, ana nan ana ta tsula tsiya a gurin taron siyasa.
Toh ita CORONA a gurin ibada, makarantu da kasuwanni ne ƙadai ta fi tafka tsiya, bata tafka tsiya a gurin taron siyasa?
ko kuma masu daure mata gindi ne su ke tafkawa guraren ibada, kasuwanni, da makarantun mu tsiya?
Ya kamata gwamnan jihar Kaduna, Mal Nasiru Elrufai da duk wani gwamnan da ya hana yin ibada a jiharsa, ya kuma ƙulle kasuwanni da su yi gaggawan gyale mutane, mu budu guraren ibadunmu da kasuwanninmu.
Sannan ita ma gwamnatin tarayya ta buɗe mana makarantunmu. Su ƙyale kowa ya ci gaba da harkar shi yadda a ka saba.