Addini

Soja Mai Ridda: Dalilin Kulle Kofur Musa Mai Wa’azin Kirista a Calabar – Rundunar Sojoji

Spread the love

Rundunar yan sojojin Najeriya sun bayyana babban dalilin da yasa suka kama gamida garƙame sojan nan Kofur Musa Adamu abisa laifin yin wa’azi da aka hango yanayi.

Rundunar ta sojin, ta shaidawa manema labarai cewar, ta garƙame sojan ne ba domin ya canja addini daga Islama zuwa Kiristanci bane a’a, sunyi haka ne domin ya karya ka’ida da tsarin gidan soja.

Hakan na zuwa ne a wani bayani da mai magana da yawun rundunar Birgediya janar Onyema Nwachukwu ya fitar.

Inda yake ƙaryata wani rahoto da wata jaridar yanar gizo-gizo ta bayyana.

Rahoton na jaridar ya nuna cewa, sojan an kulle shi a ɗakin masu laifi ne na tsawon kwanaki 45 tare da tsayar masa sa asusun amsar albashin sa, duk don wai saboda yayi wa’azi azo akan a bautawa Yesu Almasihu, kwanaki kaɗan bayan yayi ridda.

Bayanin da rundunar ta saki ya bayyana rahoton da ƙage, da kuma rashin iya fassara abinda yake faruwa cikin wani salo na ƙarya da kuma nuna ɓangaranci na addini.

Rahoton yace ba wani abu bane face ƙoƙarin wasu ɓata gari da suke don kawo ruɗani a rundunar sojojin Najeriya ta hanyar kawo abinda zai kawar da hankalin hukumar daga abubuwa masu muhimmanci.

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito bayanin ya ƙara da cewa:

Domin cire tantama, Kofur Musa Adamu, turashi wani aiki akayi, sai aka ganshi yana wa’azi a kafafen sadarwa na zamani wanda hakan ya saɓa da dokokin zaratan sojojin Najeriya.”

Bayanin yaci gaba da cewa:

Hakan yasa muka gayyace shi domin amsa tambayoyi daga mahukunta. Maimakon yazo ya amsa tambayoyin, sai muka neme shi muka rasa na wata shida da rabi, wanda hakan yasa muka saka shi a cikin tsarin AWOL, na waɗanda ke guduwa daga aiki ba izini.”

Bayanin yace kuma, a ƙaida, idan har soja yayi kwana 7 baya wajen aiki, dokar su tabada dama a tsayar masa da albashin sa.

Ya kuma ƙaryata karairayi da rahotanni suka dinga nunawa na kafafen sadarwa na zamani da yace an hana shi albashi ne saboda yayi da’awa ayi addinin Kirista saboda ya canja addini daga Musulunci.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button