Tsaro
Sojoji da boko haram sunyi luguden wuta
Majiyar ta tabbatar mana da cewa an kashe mayakan Boko Haram bakwai a yayin harin wanda ya kwashe awanni biyu. Haka kuma an kashe wani yaro farar hula mai shekaru biyar, wanda harsashi ya tashi. SaharaReporters sun tattaro bayanai cewa gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, yana garin Damasak a ranar Laraba don rarraba kayan agaji ga mutanen da suka rasa muhallinsu a garin. Rikicin Boko Haram ya haddasa mutuwar mutane sama da 35,000 tun daga shekarar 2009. Kungiyar ta’addanci tana son khalifancin Musulunci a Arewacin Najeriya. Duk da haka, an an dakile ayyukan ta a jihohin na Arewa maso Gabas guda uku, wato Adamawa, Borno da kuma Yobe saboda kokarin hukumomin tsaro.