Labarai

Sojoji sun budewa Farar hula wuta a Borno

Spread the love

Wanda ake zargin Sojoji ne sun harbi wani Farar hula a Maiduguri Dake  jihar Borno jaridar Mikiya ta samu labarin yadda wasu masu Kama da Sojoji Suka budewa wasu matasa Cikin a daidai sahu wuta a jihar Borno matashin Mai suna Bukari Wanda Yana daga Cikin wa’yanda aka harba Jaridar Mikiya ta samu zantawa dashi ya Kuma tabbatar Mana da faruwar Al’amarin da yake labartawa mikiya yadda Abin ya faru…


Yace kawai mun tashi a wajen aiki a Ranar 15 ga watan da muke Ciki da misalin karfe 07:30Pm sai na tare  daidai sahu Zan tafi gida muna Cikin tafiya sai muka hango Sojoji motoci sunyi fakim wani cikinmu yana so ya sauka sai mukace ya tsaya mu wuce  wajen sojojin tunda layin wucewa yazo kanmu Bayan munzo daidai Galadima jection sai Suka tsaidamu suna rike da bindiga kawai sai mukaga Daya yayi harbi Cikin adaidai sahun Ina fita da gudu sai na Fadi Jama’a Suka taho Suka taimakeni Suka sakani Cikin adaidai sahu Suma kuma Sojojin sai Suka shigo Cikin keke naped din Suka bimu kamar zasu kaimu Asibiti mun kusa Asibiti shine suka gudu.


Yanzu Haka Ina kwance a babban Asibitin Borno Genaral Hospital sun harbeni a kafa Ina fama da azabar ciwo Babu Wanda ya taimaka mani Inji Bukari
 jaridar Mikiya zata cigaba da bibiyar lamuran…

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button