Tsaro

Sojoji sun cafke mutane 30 da ake zargi da wawushe gidan Yakubu Dogara.

Spread the love

Rundunar tsaro ta musamman, Operation Safe Haven (OPSH), da ke tabbatar da zaman lafiya a jihar Filato ta cafke wasu mutane 30 da ake zargi da lalatawa da kuma kwasar dukiya mai tsoka a gidan tsohon Kakakin Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara da ke Jos.

Kwamandan rundunar aiki Maj.-Gen. Chukwuemeka Okonkwo ya gabatar da wadanda ake zargin a gaban manema labarai ranar Lahadi a Jos.

A cewarsa, an kame maza 13 da mata 17 a gidan.

Okonkwo, wanda ya bayyana lamarin a matsayin laifi, ya ce wadanda ake zargin sun karya dokar hana fita ta sa’o’i 24 da gwamnati ta sanya a wasu sassan jihar.

“Wannan zagon kasa ne kawai. Barnata dukiyar gwamnati da ta wasu mutane masu zaman kansu laifi ne.

“Don haka, ba za mu iya zama mu kalli wasu bata gari suna wawure dukiyoyin jama’a da na masu zaman kansu a jihar ba,” inji shi.

Kwamandan ya ce za a mika wadanda ake zargin ga hukumar da ta dace don hukunta su.

Kayayyakin da aka kwato daga hannun wadanda ake zargin sun hada da: injin nika guda takwas, babura masu taya mara kyau guda biyu, injin mai taya uku da kuma kayan sawa guda daya.

A baya rundunar ta kama wasu mutane 123 da ake zargi da lalatawa da kuma kwasar ganima daga kamfanoni masu zaman kansu da kadarorin gwamnati a cikin garin Jos.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button