Tsaro

Sojoji sun kashe mayakan ISWAP 41 – ciki har da babban kwamanda a Borno

Spread the love

Dakarun ‘Operation Hadin Kai’ da ‘Civilian Joint Task Force’ (CJTF) sun kashe mayakan ‘yan ta’addan Islamic State West Africa Province (ISWAP) 41 a karamar hukumar Dikwa ta jihar Borno.

A cewar Zagazola Makama, wani bugu na yaki da ‘yan tada kayar baya da ya mayar da hankali kan yankin tafkin Chadi, Abu Zahra, babban kwamandan ISWAP na daga cikin mayakan da aka kashe.

Zagazola ya ce farmakin da Shaibu Waidi, babban kwamandan runduna ta 7 ya jagoranta, yana mayar da martani ne ga hare-haren da ISWAP suka kai a kauyen Mukdolo.

“Kwamandan ‘yan ta’addan, (Amir Jaysh), tare da wasu ‘yan tsiraru rahotanni sun ce sun gudu a cikin rudani saboda karfin wuta da sojoji suka samu, inda suka yi watsi da dukiyoyinsu na miliyoyin naira a gidan ‘yan ta’addan da sojoji suka lalata. ” inji jaridar.

An samu nasarar kwato wata motar bindigu, babura uku, da kuma wasu kayan aikin soja da dama daga hannun maharan.

A halin da ake ciki kuma, an yi wani biki a Konduga da ke jihar Borno a ranar Asabar bayan da sojojin bataliya ta 222 suka fatattaki mayakan ISWAP.

An ce maharan sun yi luguden wuta mai tsanani kan sojojin da ke gadin kauyen da misalin karfe 6:45 na yammacin ranar Asabar.

A martanin da sojojin suka yi, sun yi artabu da mayakan da bindiga wanda ya yi sanadin mutuwar da dama daga cikinsu yayin da wasu kuma suka gudu daga wurin.

“Mun kwato motarsu, bindigar kakkabo jirgin da dukkan makamansu. Ba a samu asarar rai ba a bangaren sojojin a yayin harin,” wata majiyar soja ta shaida wa jaridar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button