Tsaro

Sojoji sun kashe yan ta’adda, sun kuma kubutar da mutane 28 da akayi garkuwa dasu a jihar Katsina

Spread the love

Rundunar Sojojin Nageriya Operation Sahel Sanity sun kubutar da mutane 14 da suka hada da mata biyu da ‘yan ta’adda suka sace a yankunan Faskari da Mararaban Kawaye da ke cikin jihar Katsina.

Jami’an sun kuma kubutar da fasinjojin bus 14 wadanda ‘yan ta’adda suka sace a hanyar Dutsinma-Yantumaki a ranar 9 ga Satumba.

Wadanda lamarin ya rutsa da su, wadanda ke kan hanya a cikin motar kasuwanci sun ci karo da ‘yan ta’addar ne wadanda suka karkatar da motarsu a kokarinsu na yin garkuwa da su.

Amma, bayan wani bayanin sirri, sojojin sun yi sauri suka bi ‘yan ta’addan suka tilasta su suka bar motar tare da fasinjoji 14 da aka kubutar lafiya.

Ma’aikatan sun kuma kwato shanu 40 da aka sace a yankin Kwanar Maje wadanda rahotanni suka ce an maido wa masu su.

A cewar wata sanarwa a ranar Litinin daga mukaddashin Daraktan ruko na Defense Media Operations, Brig. Janar Bernard Onyeuko, sojojin da aka tura Daki Takwas sun tare kuma sun kama mambobin Yansakai 17 dauke da makamai a kan babura bakwai a kauyen Danmarke da ke karamar hukumar Bukkuyum ta Jihar Zamfara, a ranar 8 ga Satumba.

Binciken farko ya nuna cewa wadanda ake zargin sun fito ne daga Maga a jihar Kebbi. Kayayyakin da aka kwato daga hannunsu sun hada da bindigogi guda 12, babura bakwai da layu. Rundunar ta ce ana cigaba da tuhumar wadanda ake zargin.

Rund ta kuma ce wani shugaban yan fashin da aka bayyana da suna Sada ya mika wuya ga sojoji a Forward Operation Base Dansadau kuma ya mika bindigogin AK47 uku, karamar bindiga daya da kuma harsashi biyu.

Rundunar ta kara da cewa sojojin da ke gudanar da aikin sintiri a yankin Shekewa sun lalata sansanonin ‘yan ta’adda da dama tare da cafke wasu mutane uku da ake zargin’ yan fashi ne, mutanen sune Adamu Musa, Hassan Bello da Rabiu Salisu.

Rundunar ta ce an kashe wani da ake zargin dan ta’adda ne yayin da yake kokarin tserewa a kan babur, sannan kuma sojojin da ke amsa kiran gaggawa sun dakile wani yunkurin da ‘yan ta’addan suka yi na kai hari a kauyen Magami.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button