Tsaro

Sojoji sun kashe ‘yan ta’addan Boko Haram da yawa a dajin Sambisa.

Spread the love

An aiwatar da aikin ne tare da jiragen yakin sojin saman Najeriya (NAF).

Rundunar Sojin sama na Operation Lafiya Dole sun lalata maboyar ‘yan ta’addan Boko Haram.

Hedikwatar Tsaro (DHQ) ta sanar a ranar Talata, 29 ga Disamba, 2020 cewa an kashe wasu ‘yan ta’addan Boko Haram da ba a tantance adadinsu ba.

Mai magana da yawun DHQ, Manjo-Janar John Enenche ya ce, rudunar ta sama ta gudanar da aikin ne daga Rundunar Sojin Sama ta Operation Lafiya Dole a ranar Litinin, 28 ga Disamba.

An gudanar da aikin ne a yankin ‘S’ da ke tsakiyar dajin Sambisa da ke jihar Borno.

An aiwatar da harin na sama ne tare da jiragen yakin Sojan Sama na Najeriya (NAF) bayan rahotannin sirri sun gano ‘yan ta’addan a matsayin wadanda ke da alhakin hare-hare na baya-bayan nan a yankin kudancin Borno da arewacin Adamawa.

“Jirgin saman NAF din ya yi wa yankin kawanya a jere, wanda ya kai ga lalata wasu gine-ginensu da shagunansu na kayan aiki, gami da wani tashar da ke dauke da bindigogin kakkabo jiragen sama yayin da‘ yan ta’addan ke harbin jirgin NAF.

Enenche ya ce “an kuma kashe masu tayar da kayar baya da dama a yayin aikin.”

Kungiyar Boko Haram ta kashe sama da mutane 30,000 tare da raba miliyoyi da muhallansu a yankin arewa maso gabas a cikin shekaru goma da suka gabata.

Daga Sabiu Danmudi Alkanawi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button