Tsaro

Sojoji Sun kwato Shanu 17 Da Kama Yan Bindiga Da Dama

Spread the love

Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe

Sojojin Najeriya sun bayyana wasu daga cikin nasarorin da suka samu a baya bayan nan kan wasu ‘yan bindiga da ke yawo a yankin Arewa maso Yamma.

Sojoji sun kwato shanu 17 daga hannun barayin shanu a kauyen Dogon Ruwa. An dawo da shanun daga hannun wasu ‘yan fashin da suka yi watsi da su kuma suka gudu.

A wata sanarwa da kakakin rundunar, Bernard Onyeuko ya sanyawa hannu,

“Babban hafsan sojojin, Laftanar Janar Tukur Yusufu Buratai ya yabawa sojojin bisa ga nasarar da suka samu, da kuma juriya da suka yi,” Onyeuko ya ce a cikin sanarwar sa.

“Ya gargadesu kar su huta game da yakin, Ya kuma kara tabbatar wa jama’ar yankin Arewa maso Yamma game da kudurin Najeriya na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin da ke yankin. ”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button