Labarai

Sojoji sun Samu Nasara akan wasu Yanta’ada a Zamfara.

Spread the love

Hadin Gwaiwar Rundunar soji masu yaki da muggan laifuka sun samu gagarumar Nasara akan wasu Yan ta’adda masu zalunta Alummah wadanda basu yarda da Sulhuba.

1 A Ranar 21/11/2020 a Yankin Galadi da ke cikin karamar Hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara, Jami’an soji sun halaka Yan ta’adda 2 tare da samun Bindigogin su 2 kira AK 47.

  1. Haka Kuma a Yankin Sabon Tunga da Tamuske, Jami’an Tsaron sojin sun hallaka Yan Bindiga da dama tare da kubutar da mutane 3 da sukayi Garkuwa da su. A Garin Dutsen Emai Sojojin kundumbala sun hallaka Yan Bindiga da dama ta hanyar Amfani da jirgin yaki.
  2. Rana 21/ 11/ 2020, Runduna soji a Garin Gobirawa ta Kara samun Nasara Hallaka Yan Bingiga 6 tare da samun Bindigogi 4 kira AK 47, da Bindigar Gargajiya 3 da Babur 2.
  3. A Garin Kadauri da ke cikin karama Hukuma Maru, Jihar Zamfara, jami’an Tsaron sojin sun Kama mutane 11 da ake zargin su da aikin hako ma’adanai ba’a bisa ka’ida ba, tuni dai sojoji su ka mika su ga Hukumar da ta dace Dan bincike.
  4. Jami’an Tsaron soji da ke aiki a garin kotarkoshi da ke cikin Karamar Hukumar Bungudu ta gabas,sunyi Nasara cafke wani da su ke nema ruwa jallo Mai suna Shafiu Suleman a cikin Kasuwa garin, Bincike ya Nuna Yanada hannu a cikin wasu hare-Hare da yankunan sukayi famada su a kwanan baya.

Hakan ta sake faruwa a Gidan Ruwa kusa da Rukudawa da ke Zurmi, jihar Zamfara, rana 22/11/ 2020, jami’an Tsaron soji sun Kai samame a yankin a lokacin samamen. Yan Bindigar sun hango sojoji zuwa inda suka ranta a cikin na kare, duk da haka sojoji sunyi amfani da dubarun yaki sun hallaka Dan Bindiga daya tare samun Bindigar sa, AK 47 1 ,Hadi da Kama 2 daga cikin su.

A Garin kurfi da ke cikin jihar Katsina, Rana 22 11/ 2020, jami’an Tsaron sojin sunyi Nasara kame wani shugaban Yan ta’adda Wanda Yana cikin.

Kamar yadda Maj. Gen. John Enenche
Shugaban watsa labarai na Runduna soji ta kasa ya bayyana
B. Lawal ya wallafa

Allah ya kara bamu Zaman lafiya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button