Sojojin Chadi Sun Ragargaji ‘Yan Boko Haram.
Sojojin Chadi sun kashe ‘yan Boko Haram 20 tare da ceto fararen hula 12, ciki har da yara tara, da aka yi garkuwa da su a yankin tafkin Chadi inda iyakokin kasashe da dama ke haduwa, in ji gwamnati a ranar Juma’a.
Kungiyar masu da’awar jihadi, wacce ta samo asali daga Najeriya a shekarar 2009, ta kafa sansanoni a kan wasu tsibirai da ke kan tabkin Chadi, fadada mai fadi a kan iyakar tsakanin Najeriya, Chadi, Nijar, da Kamaru.
Ta zafafa kai hare-hare a yankin a ‘yan watannin nan.
A ranar 17 ga watan Satumba, mayakan Boko Haram sun kai hari kan wani kauye a yankin da ke fama da tashin hankali tare da yin garkuwa da fararen hular, kamar yadda Ministan Sadarwa kuma kakakin gwamnati Cherif Mahamat Zene ya shaida wa kamfanin dillacin labaran Faransa.
Sojojin sun fatattaki maharan kuma sun far musu a ranar Alhamis a Barkalam, kusa da kan iyaka da Najeriya, ya ce, “sun kashe ‘yan ta’adda 15” sannan “sun kubutar da fararen hula 12.”
Ba da jimawa ba, sai aka sake yin wani artabu a Bilabrim inda aka kashe mayakan Boko Haram biyar tare da jikkata sojojin Chadi biyu.
Sojojin Chadi sun kaddamar da farmaki kan kungiyar Boko Haram a watan Afrilu bayan mutuwar wasu sojoji 100 a wani hari da kungiyar ta kai wa daya daga cikin sansanoninsu.
Daga nan Shugaba Idriss Deby ya yi ikirarin cewa ya kori masu jihadi.
Amma ana ci gaba da kai hare-hare duk da aikin sojan.
A cikin Lardin Tafkin Chadi, fiye da mutane 360,000 sun tsere daga gidajensu don kauce wa hare-hare da ma ambaliyar, a cewar Hukumar Kula da Hijira ta Duniya (IOM).
Shugaban ya yarda a farkon watan Agusta cewa “har yanzu Boko Haram za ta yi barna mai yawa” a Chadi.
Rikicin Boko Haram ya kashe mutane sama da 36,000 tare da raba sama da miliyan biyu da muhallinsu.
Tun daga lokacin rikicin ya bazu zuwa kasashen Nijar, Chadi da Kamaru.