Labarai

Sojojin Kasarmu Basu Take Hakkin Dan Adam Ba, Inji Gwamnatin Kasar Nijar.

Spread the love

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta aikewa kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya ta wata takarda dake karyata Rahoton cewa sojojin jamhuriyar Nijar din suna take hakkin bil’Adam.

Malam Musa Hankurau shine ministan harkokin wajen kasar Nijar ya aike da wasikar a ga kwamitin.

Yana mai ikirarin cewa wannan rahoto karya ne, kuma kuma rahoto ne da bashida kamshin gaskiya a ciki.

Ana dai zargin sojojin Jamhuriyar Nijar ta cin zarafin al’umma a yankunan Diffa, dakuma kasar Mali.

A cikin wasikar Hankurau ya nunarda cewa babu sojojin Jamhuriyar Nijar a yankin Diffa a lokacinda aka fitarda wannan rahoto.

Jamhuriyar nijar ta tabbatarda cewa itafa a shirye take ga kowacce Kungiya ta Kasar waje dake bukatar gudanarda bincike akan wannan Lamari.

Kungiyar kare hakkin bil’adam ta Amnesty International ta zargi sojojin kasashen yankin sahel da kisa dakuma batarda fararen hula 102 tsakanin watan Maris zuwa Afrilu a yankin inmates.

Daga Abdullahi Muhammad Maiyama

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button