Labarai

Sojojin ku ba zasu iya kamani ba ~Shekau

Spread the love

A cewar Shekau a cikin sabon bidiyon, ya yi wa sojoji barazana, inda ya bayyana cewa shi da mayakan sa sojoji baza su iya kamasu ba Kuma ko an kama su, Hakan ba zai kawo karshen yakin ba.

Ya ce, “Babu wanda zai iya kama ni. Amma idan haka nema to, ba zai kawo karshen yakin ba. ”

Idan za a tuna Sojojin Najeriya a makon da ya gabata Laraba, sun ayyana wani gungun ‘yan ta’addan Boko Haram da sauran masu tayar da kayar baya da ake nema saboda laifuka daban-daban da suka shafi tayar da kayar baya na ta’addan ci..

Anyi hakan ne a babban sansanin Chabbal da ke Maiduguri, jihar Borno a wani shiri da ya samu halartar shugaban hafsin sojin kasa, Laftanar Janar Tukur Buratai, da gwamna Babagana Zulum na Borno.

Mashahurai a cikin jerin sunayen ‘yan ta’adda sun hada da Abubakar Shekau da Abu Mus’ab Al- Barnawi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button