Sojojin Mali Sun Cimma Matsaya Kan Kafa Gwamnatin Riƙon Kwarya.
Sojojin da ke jagorantar gwamnatin Mali sun bayyana cewa za su kafa gwamnatin riƙon ƙwarya ta tsawon watanni 18 har zuwa lokacin da za a yi zaɓe a ƙasar.
Mai magana da yawun sojojin, Moussa Camara ne ya bayyana cewa wanda zai jagoranci gwamnatin riƙon ƙwaryar zai kasance ko dai soja ko kuma farar hula.
A kwanaki uku da suka wuce, sojojin da ke jagorantar gwamnatin ƙasar na ta tattaunawa da ‘yan adawa da kuma ƙungiyoyi masu zaman kansu a Bamako babban birnin ƙasar.
Sai dai tun a kwanakin baya bayan juyin mulkin da aka yi wa Tsohon Shugaban ƙasar Ibrahim Boubacar Keita a watan Agusta, Shugabannin Ƙasashen Yammacin Afrika sun buƙaci a miƙa mulkin ƙasar cikin gaggawa ga farar hula.
Juyin mulkin ƙasar ya biyo bayan zanga-zangar da ‘yan adawa suka shafe tsawon lokaci suna yi inda suka zargi tsohon shugaban ƙasar da gaza shawo kan matsalar tsaro da kuma jefa tattalin arziƙin ƙasar cikin halin ha’ula’i.
Daga Amir sufi