Tsaro

Sojojin Nageriya sun kashe ‘yan Bindiga mutun Hudu a jihar kaduna.

Spread the love

Jami’an tsaro a Kaduna sun tabbatar da kashe akalla ‘yan bindiga hudu a wani kwanton bauna da aka yi a kananan hukumomin Chikun da Birnin Gwari na jihar.

An gano bindigogi uku da gatari daya daga hannun ‘yan bindigar wadanda suke cikin kungiyar’ yan ta’addan da ke addabar sassan jihar.
Kwamishinan tsaron cikin gida da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, wanda ya tabbatar da kisan a cikin wata sanarwa, ya ce bisa ga bayanin da suka samu daga rundunar Operation Thunder Strike (OPTS), an samu bayanan sirri kan ‘yan bindigar da suka yi kaura daga kauyen Katika zuwa Antenna a Chikun LGA. Aruwan ya ce sojoji sun yi kwanton bauna a kauyen Antenna, kuma yayin da ‘yan fashin suka matso, sai suka bude musu wuta suka kashe hudu a wurin.

Ya kara da cewa an kara kakkabe wasu ‘yan ta’addan a yayin samame ta sama da aka gudanar a wuraren da suke a kananan hukumomin Chikun da Birnin Gwari.

Ya ce gwamna Nasir el-Rufai ya yaba wa sojojin saboda matakin gaggawa da suka kai ga nasarar fatattakar ‘yan bindigar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button