Labarai

Sojojin Nageriya zasu samu taimakon Dollar amurka Bilyan Daya $1bn daga gwamnatin Qatar.

Spread the love

Sojojin Najeriya, Navy, ‘Yan Sanda da Sojan Sama, da sauran hukumomin tsaro nan ba da dadewa ba za su samu kusan dala biliyan 1 daga gwamnatin Qatar da nufin sayo kayayyakin kimiyyar zamani, Afirka-Global Empowerment and Development Network (AGED-Network) ta bayyana .

Shugaban kungiyar ta AGED-Network, Dr Bala Kontagora, ya bayyana hakan ga manema labarai a Abuja yayin taron kasa na yini daya kan rawar da hukumomin tsaro na Nijeriya suka taka
Kontagora ya ce neman kudi daga gwamnatin Qatar ta hanyar Sheikh (Dr.) Badr Al-Hajri, da sauran kasashen duniya don wadata ‘yan sanda da sauran hukumomi da kayan aiki na zamani ya zama tilas saboda karuwar kalubalen tsaro a fadin kasar.
Ya ce, “Mun sanya hannu kan Yarjejeniyar Fahimta (MoU) tare da Kwalejin Tsaro ta Kasa ta hanyar cibiyar don dabarun bincike da nazari da babbar manufar ci gaba da kawo sauye-sauye da hadin kan bangarorin tsaro a tsakanin dukkan hukumomin tsaro.

“Kokarin da muke yi ya bamu damar samun dala biliyan daya daga  gwamnatin Qatar ta hanyar alakarmu ta musamman da kwararru tare da Sheikh (Dr.) Badr Al-Hajri, wanda da kansa ya ziyarci AGED-Network a Abuja.”

Ya kara da cewa tare da darussan da aka koya daga barazanar tsaro na baya-bayan nan, gami da zanga-zangar da aka kammala a duk fadin kasar #EndSARS da kuma tunkarar rikicin bayan COVID, dole jami’an tsaro su sake ninka kokarinsu

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button