Tsaro

Sojojin Najeriya Sun Dakume Masu Garkuwa Da Mutane 24 A Jihar Ondo.

Spread the love

Daga Miftahu Ahmad Panda.

Mayakan Sojan Najeriya ne dai Sukayi Nasarar Dakume Masu Garkuwa Da Mutanen da Yawansu yakai Mutum 24 a Yankunan Awo da Akoko dake Jihar Ondo, a Lokacin dasuka kai Wani Sumame.

Sumamen wanda Aka Kai Makonni Biyu da Suka Gabata, Biyo Bayan Awun Gaba da Masu Garkuwa Da Mutanen Sukayi da Jami’an Rundunar Sojojin Kasarnan Mutum Biyu, Da suka Hadarda Jami’i a Rundunar Sojojin Ruwa, da kuma Kaftin a Rundunar Sojojin Kasa, a Yankunan Guda Biyu.

Sannan daga Cikin Al’umar da Masu Garkuwa Da Mutanen Sukayi Garkuwa Dasu sun Hadarda Matafiyan da akayi Garkuwa Dasu akan Hanyar Lagos Zuwa Abuja, Wanda suma Akayi Garkuwa Dasu a Lokaci Guda.

Shugaban Rundunar Sojojin Kasa ta Najeriya (COAS), Lieutenant Janar Tukur Yusuf Burtai, Shine yasanar da Dakume Masu Garkuwa Da Mutanen 24 da Rundunarsu tayi, a Lokacin da ya ziyarci Olowo dake Owo, Inda yakai Gaisuwa Fadar Oba Ajibade Gbadegesin Ogunoye na III dake Jihar ta Ondo.

Janar Burtai, Wanda Kwamandan 32 Artillery Brigade, Janar Zakan Abubakar, ya wakilta, ya Bayyana cewar Rundunar Sojojin Najeriya bazata Gajiyaba Wajen Ganin ta Cigaba da Kare Rayuka Tareda Dukiyoyin Al’ummar Jihar ta Ondo,

Yakara dacewar sun tsaurara Matakan Tsaro a Yankunan Owo Zuwa Oba Akoko, Wanda hakannema Yayi Sanadin Wannan Gagarumar Nasarar da Suka Samu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button