Sojojin Najeriya Sunyi Ramuwar Gayya Akan ‘Yan Kungiyar Boko Haram Da Yammancin Yau..
Rudunar sojojin Najeriya ta operation lafiya dole sun kashe ‘yan kungiyar boko haram sama da guda Ashirin 20 kuma sun raunata wasu da dama, sannan sun kwato motar yaki Daga hannun ‘yan ta addan a jihar Borno.
Rundunar sojojin sun yiwa ‘yan ta’addan wani kwanton bauna ne yayin da suka sami bayanan sirri a lokacin da ‘yan ta’addan sukai shirin kawo wani mummunan hari a garin Bama.
Bukar Sale wani dattijo dake sana’ar saran itace ya bada labarin cewa yana cikin tafiya ya hangi wucewar gungun sojojin a guje har wasu daga cikin sojojin suna nuna masa alama daga nesa cewa yayi sauri ya koma baya hanyar bata da kyau.
Bukar Sale ya kara da cewa wucewar babu dadewa se yaga suna barin wuta babu kakkautawa.
Bukar yace be karasa inda ya dosa don tsira ba seya ringa ganin sojojin suna ta dawowa gawawwakin ‘yan ta addan boko haram din Abin kyawun gani.
Daga Kabiru Ado Muhd.