Sojojin sama sun Kashe ‘yan ta’adda a jihar katsina
Wata sanarwa da mai kula da Sashen Kafafen Yada Labarai na Rundunar, Manjo Janar John Eneche ya fitar, ta ce an kai farmakin ne da zummar kakkabe ‘yan bindigar a maboyarsu.
Manjo Eneche ya ce, sun yi amfani da bayanan sirrin da suka tattara wajen zakulo maboyar tsagerun domin karya lagonsu, yana mai cewa, dakarun sun yi amfani da jiragen yaki wajen kai farmaki kan sansanoni 10 na ‘yan bindigar tare da raba su da makamansu .
Wuraren da sojojin suka kai harin sun hada da Dutsen Asolo da Birnin Kogo da ke jihar Katsina da kuma sansanin Dogo Gede da ke Dajin Kwayanbana a jihar Zamfara a cewar sanarwar da Eneche ya fitar.
Wannan na zuwa a daidai lokacin da ‘yan bindiga suka addabi wurare da dama a sassan arewacin Najeriya, inda suke kaddamar da munanan hare-haren kan mutane tare da kona gidajensu da kuma sace dukiyoyinsu baya ga yi musu yankar rago a wasu lokutan.