Sojojin Saman Kasar Nan Sun Hallaka ‘Yan Bindiga a Kaduna.
Hedikwatar tsaro ta Kasa ta ce sojojin sama karkashin, Operation Thunder Strike, ta kashe wasu yan’bindiga da yawa a cikin wani daji dake yankin Kuzo a Jahar Kaduna.
Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar tsaro, Manjo John Enenche, ya bayyana cewa, ta jiragen sama aka kaiwa masu yan ta’addan hari a ranar Asabar.
Cikin sanarwar da Enenche ya fitar a Jiya Lahadi ya ce, an kashe ya ta’addan ne a lokacin da suke yunkurin kwashe daruruwan dabbobin da suka sata a yankin.
Inda yace, jirgin sama mai saukar Ungulu na rundunar sojan sama ta Najeriya, na kan aikin leken asiri a yakin ne ya hango ‘Yan bindigar tare da dabbobin da suka sata a cikin wani budadden shinge.
“Jirgin sama mai saukar ungulu yana sintiri a yakin da aka kai hari wanda hakan ya kai ga samun nasarar kashe ‘yan ta’addan da dama.”
Sai dai rahotun bai bayyana adadin ‘yan ta’addan da aka kashe ba.