Sowore zai maka Rundunar ‘yan sanda Nageriya a Kotun Kan Azabtar dashi da sukayi a Abuja ~Lauya Falana
Shahararren lauya kuma dan gwagwarmaya, Femi Falana a ranar Asabar ya bayyana cewa ya samu umarni daga dakaren na kungiyar #RevolutionNow, Mista Omoyele Sowore, da ya kai karar rundunar ‘yan sanda ta Najeriya akan azabtarwar da sukayi Masa.
Wannan ya na kunshe ne a cikin wata sanarwa da fitaccen lauyan ya fitar.
A cewar Femi Falana, wanda yake karewa an wulakanta shi, an azabtar da shi, an kuma sanya shi cikin yanayin cin mutuncin mutum wanda ya sabawa dokar hana cin zarafin mutane.
Ku tuna cewa Omoyele Sowore an kama shi ne a jajibirin sabuwar shekara saboda jagorantar zanga-zangar adawa da Gwamnatin Tarayya a Abuja.
Falana ya ce: “ Tun da ‘yan sanda sun keta hakkin Mista Sowore na rashin mutunci, muna da umarnin da ya ba mu damar gurfanar da shi a kan dukkan jami’an da suka yi masa azaba ta jiki da ta kwakwalwa wanda hakan ya saba wa wasika da ruhin tanadin. na dokar hana azabtarwa ta shekarar 2017. ”