Su Waye Masana Kimiyyar Musulunci? (1)

Ranar 2 ga watan January na wannan shekara ta 2020 ta kasance rana mafi muni ga ilahirin kasar Iran da kawayenta da sauran mutanen duniya da sukayi jimamin kisan gillar da Amurka tayi wa Qassim Sulaimani. A wannan rana ne nayi rubutu kan dalilin da yasa kimiyyar kasar Farisa (Persia) bata cigaba ba, dalilai mafiya rinjaye sune sanya mata takunkumin da kasashen yamma da abokan hamayyarta na gabas ta tsakiya sukayi. Saboda haka a yau duniyar musulunci bata cika tunawa da manyan masana kimiyyarsu ba, da kuma gudummawar da suka bawa kimiyyar zamani. Sai dai a kullum tunawa mukeyi da gudummawar da su Albert Einstein, Galileo, Lamataire, Hubble da sauransu suka bawa kimiyya. Mun manta da hazikan kakaninmu da sukayi ruwa da tsaki don ganin mun amfana, amma sai dai kash! Kimiyyar bata hannunmu har yanzu.
A yau kudiri na shine kawo sunayensu da gudummawar da suka bawa kimiyya wanda har yanzu, kuma har gobe mutanen duniya suna cin moriyarsu. Har ila yau, zan so yin bayani ko kadan ne dangane da fasaharsu da kasashen yamma suka sata suka mayar dasu nasu. Bugu da kari, a cikin wannan rubutun dai zan hada da manyan masana kimiyyar musulunci a dunkule, shiyasa na sanyawa rubutun taken “Su Waye Masana Kimiyyar Musulunci?” amma saboda hazikanci, jajircewa da kuma babbar gudummawar da masana kimiyyar Farisa suka bawa kimiyyar zamani da musulunci wanda har abada baza’a taba mantawa da su ba yasa na yi wannan rubutu a sama don nuna fifiko.
Wato anan idan nace “masana kimiyyar musulunci” ina nufin kwararrun masana kimiyya wadanda sukayi ruwa-da-tsaki wajen ganin sun samar da gudummawa mai tarin yawa ga kimiyya domin gina ta, sannan wadannan masana kimiyya sun kasance musulmai ne, basa kuma aibata wani cigaba ko bincike da suka samu ta bangaren kimiyya matukar bai ci karo da addinin musulunci ba. Wadannan hazikan masana sun dukufa wajen ganin sun gina fannin kimiyya na chemistry, physics, medicine, astronomy, biology, mathematics da sauransu tun daga karni na bakwai (7th century) har zuwa karni na goma sha tara (19th century), wanda daga nan ne duniyar masana kimiyya ta hade wuri guda kama daga musulmai, yahudawa, kiristoci, da sauran addinai da ma wadanda basu da addini.
Mu hadu a kasha na biyu…
Daga Marubuci:
Mohiddeen Ahmad
Wanda Ya Tace: Ismail Aliyu Ubale