Rahotanni

Subhanallah: Tankar Mai Ta Shiga Masallaci Ta Kama Da wuta Ta Kuma Kone Shuguna Da Gidaje A Neja.

Spread the love

Rundunar ‘yan sanda a Neja ta ce wata tankar dakon mai dauke da man wacce ta zo daga Minna zuwa Suleja ta tsallake hanya sannan ta afka cikin wani Masallaci da ke Lambata a karamar hukumar Gurara ta kone Shaguna 52 da gidaje 10.

kwamishinan ‘yan sanda na jihar Adamu Usman, ya tabbatar da afkuwar lamarin a hirar sa da manema labarai yau Litinin a minna.

Usman ya ce “hatsarin, wanda ya faru da misalin karfe 22:45 na daren jiya Lahadi, ya haifar da konewar wata wata Tankar mai da kuma wata motar da ke dauke da kayayyaki.

“Tun daga lokacin muka fara bincike tare da gargadin direbobin manyan motocin da su guji daukar mutane a babbar mota saboda irin wadannan motocin ba na fasinjoji ba ne,” in ji shi.

Usman “ya ce ‘yan sanda da ma’aikatan kashe gobara sun yi iya bakin kokarinsu

Ibrahim Maje, wani mazaunin Lambata, ya ce babu hasarar rai, sai dai Mutane da dama sun samu Raunuka sakamakon Gudun Ceton Ransu daga gobarar.

Daga Ahmed T. Adam Bagas

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button