Mata iyayenmu

Sun Mata Fyade Sun Jefar da Gawar Ta A Masallaci….

Spread the love

A Ranar Juma’a da Ta gabata ne aka Tsinci Gawar wata Yarinya a Wani Masallaci a Kaduna, Lamarin Yafarune a Wani Masallacine a Unguwar Kurmin Mashi dake Karamar Hukumar Kaduna ta Kudu.

Kwamishiniyar Kula da Harkokin Mata da Jindadin al’umma ta Jahar Kaduna Hajiya Hafsa Baba ce Tace Bayan Gwaji da Aka yiwa Gawar Yarinya Mai Shekaru 6 Likitoci Sun Ce An mata Fyade ne Ta Mutu san nan aka Yadda Ita a Cikin Masallaci.

Mahaifin Yarinyar Malam. Ya’u Abdullahi Ya ce Tabbas Yarin tana Wasa A Cikin gida Kawai Ba’asan ta fitaba Ya Dawo Daga Masallaci akace Ba’a Gantaba, daga Karshe Dai Sai Kawai aka Kirashi Akace Anga Gawar Yarsa a Masallaci.

Sai dai Kawo Yanzu Ba’a Samu wanda Yayi Wannan Aika Aikar ba, Amma Hukumomi na Gudanar da Bincike kan Wanda Ya Aikata Mummunan Al’amarin.

Allah ya Kyauta.

Daga Ahmed T. Adam Bagas

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button