Sunce abba Kyari karya yake film yake shirya..

Spread the love

Wannan rubutu daga shafin marubuci m inuwa MH yake inda yake cewa…

Ni dai a iya sanina ban san iyakar barayi Azzalumai ‘Yan ta’adda maciya amanar kasa da wannan bawan allah ya kamata ba,
na gani na sheda da idona ya shiga dare da rana tare da dukan ruwan sama ya kyale iyalansa cikin kadaici dukda cewa yakasance iyalansa suna maradinsa
Suna Bukatarsa a tare dasu amma wannan bawan allah ya zabi ya bautama kasarsa akan komai ya shiga daji ya shiga birni da kauye
domin yaki da ‘yan ta’adda,
ko su kansu ‘yan ta’addar tsoron jin sunansa suke Musamman hanyar kano abuja kaduna, wannan bawan allah ko’ina ka shiga a Nageriya za kaji bayaninsa a bakin mutane suna yabonsa…

Abin Haushi da takaicin shine wai kawai don majalisar wakilai ta kirashi ta karramashi sai naji wasu bata gari marasa kishin kasa suna zagi suna cewa ai be kamata ba,
harma suna cewa abba kyari ai dan film ne babu wasu barayi da yake kamawa kawai daji yake shiga da Camera yana shirya Fina finansa na Yaudara, hmmmm nageriya kennan kasarmu ta hasada da bakin ciki…

Inama ace zamu samu masu shirya irin wannan film na malam abba kyari kamar mutun Dari 100 cikin ‘yan sandan Nageriya na tabbata da suma basawan cikin film din da kashinsu ya bushe da sauri…

Malam Abba muna maka addu’ar gamawa lafiya Madallah da samunka cikin ‘yan sandan Nageriya…

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *