Rahotanni

Ta fita kafin ta dawo gobara ta kashe ‘ya’yanta guda hudu..

Spread the love

“Da muka shiga sai muka tarar da gawawwakin yaran a dakin, sai banbarosu mukai” cewar wani ganau.

Lamarin ya faru ne a unguwar Kurna Asabe Babban layi titin ‘yan doya kusa da gidan kalanzir, inda wata mata ta fita ta bar ‘ya’yanta a gida domin tayo cefane, kafin ta dawo tuni gobara ta kone ‘ya’ya nata gudu hudu kurmus, wanda hakan yayi sanadiyyar rasuwarsu.

Wani ganau mai suna Ibrahim Muhammad Ya shaidawa Jaridar Mikiya cewa ya zo wucewa ne, sai yaga gobara ta tashi a gidan, sai ya shaidawa makwabtan wajen, da farko yaran sun fito suna ihu domin jama’a su taimaka musu, sai kuma suka koma dakin da wutar take ci, suka rufe kansu.”

Ya kara da cewa da suka shiga gidan sun yi ta ƙoƙarin kashe wutar. “Da muka shiga sai muka tarar da gawawwakin yaran a dakin, sai banbarosu mukai”.

Daga bisani dai jami’an hukumar kashe gobara sun isa wajen, kuma anyi nasarar kashe wutar.

Wani mazaunin gidan mai suna Malam Abdussamad ya tabbatar mana rasuwar yara guda hudu, da dan shekara tara, da dan shekara bakwai da dan shekara hudu, sai kuma karaminsu dan shekara biyu.

Malam Abdussamad ya ce ba su san musabbabin tashin gobarar ba, saboda ko wutar Nefa babu a gidan.

Sai dai kuma wata majiya ta shaidawa Jaridar Mikiya cewa Mahaifiyar yaran ta dora girki a kan Gass ne kafin ta fita, wata kila ko gas din ne musabbabin tashin gobarar.

Allah yakyauta..

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button