Ta komawa da Kwamfanin china Milyan 38m dayayi kuskuren tura Mata a maimakon dubu 38.
Wata mata ‘yar Najeriya ta samu yabo bayan ta koma da kudade da wani kamfanin kasar China ya biya a asusun ta.
Matar Mai suna Sola Ismail ta biya Naira dubu arba’in da daya kan wani kaya data yi Oda Koyaya ne Amma ba su da samfurin kayan kuma sun amince su dawo Mata da kudin ta amma sun ƙi aminta da biyan kuɗin duka.
Maimakon su biya ta N41K, sai suka ce za su dawo Mata da N38K ne kawai.
daga karshe ta amince ta karbi Naira dubu talatin da takwas din.
Duk da haka Kuma kawai sai ta samu Sakon miliyan 38.
kamfanin bisa kuskure ya ƙara sifili. Amma
Duk
da rashin jituwa da ta faru a tsakaninsu, matar ta sake mayar da kudin da suka biya bisa kuskure bayan an cire cajin banki.
Saboda abin da ta yi abin misali ne kamfanin na China ya canza sheka ya sake biyan ta cikakkiyar N41K data ke binsu.