Ta’addanci ya ragu a Nageriya, Yanzu ta’addanci na kashe mana mutun 200 a maimakon 2,600 a duk wata ~Nuhu Ribadu.
Mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu ya bayyana cewa adadin mace-macen da ke da alaka da ta’addanci a Najeriya ya ragu sosai daga kusan 2,600 a kowane wata zuwa kasa da 200 a yanzu.
Mista Ribadu ya bayyana haka ne yayin wata tattaunawa da manema labarai a wajen taron yaki da ta’addanci na kasashen Afirka da aka fara a ranar Litinin da ta gabata.
“Muna aiki kuma ina ganin mun yi aiki mai kyau. Daya daga cikin abubuwan da muka gani a matsayin manuniyar cewa al’amura sun fara raguwa misali, shi ne bindigar AK 47 da a da ake sayar da shi kasa da Naira 500,000 a bara amma yanzu ya koma Naira miliyan biyar.
“Yawancin wannan aikin yana ci gaba, amma mutane ba sa gani da gaske; muna jinjina wa dakarun mu, jami’an tsaron mu, gwamnonin mu da suke matukar kokari.
“Bambance-bambancen da ke faruwa a Najeriya shi ne dalilin da ya sa zan iya tabbatar muku cewa a cikin shekara guda da ta gabata mun rage yawan mace-mace sakamakon munanan laifuka da kuma amfani da makamai.
“A da muna rikodin 2,600 ko fiye a wata amma yanzu muna da kasa da 200 a matsakaici.
“Wannan lamari ne da ke nuna cewa muna samun sakamako kan aikin da ake yi,”