Labarai

Ta’addancin Boko Haram ya jawo mana Asarar dala Bilyan Tara $9bn a Yankin Arewa maso Gabas ~Cewar mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima.

Spread the love

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya bayyana haka a ranar Asabar a Maiduguri, ya koka kan yadda rikicin Boko Haram ya yi barna a yankin Arewa maso Gabas, da ya kai dala biliyan 9.

Ya ce: “Rikicin Boko Haram ya yi barna a yankin Arewa maso Gabas, har dala biliyan tara.

“Akwai irin wannan barna a jihohin Adamawa, Yobe, Bauchi, Gombe da Taraba. Idan da a ce za dauki Arewa maso Gabashin Najeriya a matsayin kasa, mun fi Chadi, Afganistan, Nijar talauci.”

Shettima ya yi kira ga hukumar NEDC da ta kara fadada ayyukan da take yi a yankin domin kara yawan ayyukan tituna ba tare da la’akari da matsayinsu ba.

Ya kara da cewa: “Ina so in yi kira ga hukumar NEDC da ta kara fadada ayyukan da ta ke yi don kara gudanar da ayyukan tituna a fadin yankin arewa maso gabas, wadanda suka hada da titin Gombe-Bauchi, Maiduguri-Damboa-Biu da Gujiba-Biu, da dai sauransu.

“Duk da ana daukar wadannan hanyoyin a matsayin Titin A, amma daga karshe ‘yan Najeriya za su yi amfani da su, musamman mutanen Arewa maso Gabas.”

“Arewa-maso-gabas wani nau’in launi ne, wanda ya kunshi mutane daban-daban daga bangarori daban-daban na zamantakewa da siyasa.

“Amma ina son in yaba wa gwamnoninmu kan hada wadannan runduna guda daya, ba tare da la’akari da bambance-bambancen siyasa da sauran al’amura ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button