Tsaro

Tabbas Jami’in mu dake aiki da Shugaban majalissa Gbajabiamila ya harbe mai siyar da jarida a Abuja, in ji hukumar DSS.

Spread the love

Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta mayar da martani game da harbin wani dan kasuwa mai siyar da jarida a Abuja, Ifeanyi Okereke.

Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis, a Yankin Makamai Uku lokacin da ayarin motocin Kakakin Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila ke wucewa.

A wata sanarwa da daddare daren Juma’a, Peter Afunanya, Jami’in Hulda da Jama’a na DSS, ya ce mai laifin yana daya daga cikin jami’anta da aka turawa Shugaban Majalisar a matsayin cikakken tsaro.

Kakakin ya ce kamar yadda Gbajabiamila ya riga ya fada, an dakatar da jami’in.

Afunanya ya tabbatar da cewa a matsayin wani bangare na ladabtarwa, an dauke shi an tsare.

Ya kara da cewa DSS ta bude cikakken bincike a kan lamarin tare da tabbatar da gaskiya da rikon amana.

“Ma’aikatar na jajantawa dangin mamacin. Ya yi alkawarin gudanar da cikakken bincike game da yanayin da ya haifar da mummunan lamarin kuma tabbas za ta ci gaba da hakan, ”in ji sanarwar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button