Lafiya

Tabbas Tana Da Tausayi: Aisha Buhari Ta Bukaci Gwamnati Da Ta Kashewa Talakawa Makudan Kudade…

Spread the love

Aisha Buhari Ta Bukaci Gwamnati Da Ta Ware Kudade Don Kawo Karshen Matsalar Karancin Abinci Mai Gina Jiki.

Uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ta yi kira ga masu ruwa da tsaki a tarayya da gwamnatocin jihohi da su kara kashe kudade don rigakafin da kuma magance duk nau’in cutar tamowa a kasarnan.

Wata sanarwa wacce mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai a Ofishin Uwargidan, Aliyu Abdullahi ya fitar ta ce ingantaccen abinci mai gina jiki yana karfafa tsarin garkuwar jiki don yakar yawancin cututtuka ciki har da COVID-19.

Uwargidan ta kuma yi kira ga masu ruwa da tsaki a cikin al’umma, dangi da masu kulawa da su tabbatar da cewa an ba da kayayyakin abincin da ake bukata ga yaran da ke fama da rashin abinci mai gina jiki don lafiyarsu ta ci gaba da dorewa.

Ta ce cutar sankarau ta COVID-19 ta yi nuni da karuwar bukatar kulawar duniya kan ‘tsananin Cutar tamowa (SAM).

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button