Tabbas Wannan CORONAVIRUS Zai Shafi Kayan Azumi Da Kayan Sallah ‘Yan Mata Na Wannan Shekara.
Daga Kais Dauda Sallau
Lamarin CORONAVIRUS ya jefa mutane cikin wata irin sabuwar rayuwa wacce za a ce ba’a taba ganin wani abu wanda ya birkita duniya baki daya kaman CORONAVIRUS ba a wannan zamanin.
Lamarin wannan annobar cuta CORONAVIRUS ya tilastawa mutane zama a gida saboda gudun kamuwa kokuma kara yadawar cutar ta CORONAVIRUS.
Ba shakka lamarin wannan cutar ta CORONAVIRUS zai shafi kayan azumi da kuma kayan sallah da samari suka saba yiwa ‘yan matansu duk shekara ganin ga azumin ya iso kuma ana kulle a gida.
Ba za a ce duka ‘yan matan za su rasa wannan kayan azumi da na sallah da su ka saba samu ba, akwai wadanda za su iya samu, amma kadan daga cikinsu. Domin nima tawa budurwan tana daya daga cikin wadanda ba za su samu wannan kayan ba.
Ya kamata ‘yan matan su yi la’akari da halin da ake ciki kada su matsawa samarin nasu sai sunyi abinda su ka saba yi musu duk shekara. Domin nasan mafi yawan ‘yan matan ba tausayi su ke dashi ba akan kayan sallah ko azumi sai su rabu da saurayinsu da su ka dade suna soyayya. Su ta koyaya suna son a biya musu bukatarsu duk halin da samarin ya ke ciki kokuma zai fada ciki. Tawa budurwar tana da tausayi ba za mu rabu akan kayan azumi da sallah ba.
Allah ya taimake ni tawa budurwar tana da fahimta, mun cinma matsaya da ita akan wannan shekaran an sauwake mini komai, ba sai na yi ba. Godiya na ke masoyiya ta.
Ina fatan sauran yan matan zasu bi sahun tawa budurwa, musamman ga samari marasa karfin arziki iri na. Hakan shima wani nuna karfin soyayya ne.
Kukuma samari masu gudu da zarar azumi ya iso, toh wannan karon babu gudu tunda an samu mafaka (CORONAVIRUS). Idan tayi magana zai ce haba dan Allah, kwana nawa muna gida ba mu zuwa aiki, ya kamata kema ki duba.
A baya kuwa da zarar azumi ya zo, guduwa ya ya ke yi, sai bayan sallah ya dawo idan ta ki ya garzaya ta wani guri.
‘Yan mata a rungumi kaddara. Banda korafi CORONAVIRUS ne ya kawo haka. Tattalin arzikin duniya ma ya ji a jikinsa balle na saurayinki.