Rahotanni
Takaddama a gwamnatin tarayya kan maganar bude iyakokin Najeriya.
Yayin zama domin tattaunawa game da maganar bude iyakokin Najeriya, wani tsagi na masana tattalin arzikin kasa sunce yawan karayar tattalin arzikin kasa da ake samu lokaci lokaci a Najeriya na da alaka da rufe iyakokin kasar.
A bangaren shugaba Buhari da makarrabansa kuma sun karkata akan cewa ba rufe iyakokin Najeriya bane, bullar cutar covid-19 ce ta zama barazana ga tattalin arzikin Duniya gaba daya bama Najeriya kadai ba.
Ana ci gaba da tattaunawa tare da karbar hujjoji masu karfi daga kowanne bangare, hujjar data sami rinjaye da ita za ayi aiki.
Anan aka tsaya.
Daga Kabiru Ado Muhd