Takai Ya Fita Daga Jam’iyya Mai Mukulli Ya Koma Mai Tsintsiya.
Dan takarar gwamna a jam iyar PRP a jihar kano Malam salihu sagir takai ya sanar da ficewar Sa daga jam iyar PRP zuwa jam iyar APC me mulki.
Daga Kabiru Ado Muhd.
Malam salihu sagir takai ya fice daga tsohuwar jam iyar Sa ta PRP zuwa jam iyar APC me mulki ne saboda yasamu damar yin takarar gwamnan jihar kano a shekarar 2023 me zuwa kamar yadda wasu Amintattun Sa suka sanar.
Malam salihu sagir takai yaqara da cewa yadda yake da magoya baya dayawa a jihar kano be fice daga jam iyar tasa ta PRP ba saida yaji ra ayin mabiyansa Wanda mafi yawancin su suka CE a koma APC sannan ya yanke hukuncin komawa jam iyar ta APC.
Dayake jawabi, shugaban jam iyar APC Na jihar kano Alhaji Abdullahi Abbas yace, shigar Malam salihu sagir takai jam iyar APC zata karawa jam iyar karfi duba ga yadda Malam salihu sagir takai din yake da dinbim magoya baya a duk kana nan hukumomi 44 dake jihar kano.