Labarai
Takaitattun Labarai. 03-12-2020:Shugaba Buhari ya ce ba zai kara karbar uzurin su Buratai ba (A kan tsaro).
- Shugaba Buhari ya ce ba zai kara karbar uzurin su Buratai ba (A kan tsaro).
- An fara koya wa matasa 17,000 yadda ake samun kudi da kiwon zomaye a Najeriya.
. - Interpol ta samu labarin rigakafin corona na bugi a Najeriya.
. - Shugaban Kasar Venezuela Nicolas Maduro ya bayyana cewar idan ‘yan adawar kasar suka yi nasara a zaben ‘yan majalisar dokoki da za a yi a ranar 6 ga Disamba to zai sauka daga kan mulki.
. - Shugaba Buhari ya aika da kayayyakin tallafi ga al’ummar yankin da aka yiwa manoma yankan Rago.
- Gwamnonin Najeriya sun bayyana cewa idan ba a tashi tsaye an yi da gaske ba,‘yan ta’adda da kuma sauran ‘yan bindiga za su iya tarwatsa Arewa, su lakume ta baki daya.
. - ‘Ƴan sanda sun tasa keyar Maina zuwa Najeriya, bayan an bankado inda yake boye a Nijar.
. - Burtaniya tace tana shirin fara yiwa mutane Rigakafin Allurar rigakafin Corona.
- Bola Ahmad Tinubu ya bada shawarar yadda za a kawo karshen ta’addanci a kasar nan.
- Shugaba Buhari ba zai yi Murabus ba- Inji Minista Lia Muhammad ga masu cewa shugaban yayi Murabus saboda Gazawar shi a fannin tsaro.
. - CDC Ta Amurka tace Za a fuskanci tsanani corona a wannan lokaci.
. - A 2023 Mulki ya koma kudu shine aikin hankali – Inji Ibrahim Shekarau.
Daga Bappah Haruna Bajoga.