Labarai

Takaitattun Labaran Safiyar Lahadi 10/05/2020CE – 17/0/1441AH.

Spread the love

Daga Haidar H Hasheem Kano

Hukumar NCDC ta ce masu dauke da cutar Covid-19 a Najeriya ya karu da 239, jimilla 4,151.

Farashin buhun shinkafa zai koma Naira 16,000 a Kano.

Kwalejin kimiyya da fasaha a jihar Ondo za ta fara gudanar da darussa a yanar gizo ranar 14 ga watan Mayu.

Sojojin Najeriya sun kama ‘yan kasan waje 28 da suke yi wa Boko Haram leken asiri.

Jihar Nasarawa ta mayar da jihar Katsina almajirai 204.

Covid-19: Hukumar NCDC ta ce jami’anta sun je taimako ne jihar Kogi, amma aka yi masu kora da hali.

Coronavirus: Gwamnatin Legas ta ce idan mutane ba su bi a hankali ba za ta rufe jihar gaba daya ba fita.

Jami’an tsaron kasar Turkiyya sun kubutar da Siriyawa ‘yan gudun hijira 26 a tekun Aegean.

Wata bakuwar cuta mai alaka da coronavirus ta soma halaka yara a Turai.

Mutum 500 sun kamu da cutar Coronavirus a ma’aikata daya a Ghana.

Tsohon shugaban Amurka Barack Obama ya bayyana yadda Trump yake yaki da cutar Covid-19 a matsayin wani mummunan yanayi mai rikitarwa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button