Nishadi

Talauci Da Jahilci Ne Ke Kawo Yawaitar Fyade Da Ta’addanci A Arewa, Inji Barr. Khalil Kabir Mantissa.

Spread the love

Wani Lauya Mai Zaman Kansa Mai Suna Barrister Khalil Kabir Mantissa ya ce “Talauci da Jahilci sune matsalolin da suka kawo yawaitar fyade da rashin tsaron da muke fama dasu a Arewacin Najeriya”.

Lauyan ya fadi hakan ne a yayi zantawarsu da Editan Jaridar Mikiya Sabiu Danmudi Alkanawi a garin Kano.

Barrister Khalil Kabir Mantissa ya ce “ita zuciyar Mutumin da yake zaune haka kurum babu aikin fari balle na baki masana’antar shaidan ce aciki, dole za ta yi ta saka masa abubuwa marasa kyau, wanda daga karshe shi kuma sai ya aikata abun”.

Da yake amsa tambaya akan irin hukuncin da alkalai suke yankewa akan masu fyade da ‘yan ta’adda, Mantissa ya ce “shi Alkali ba shi da ikon yanke hukuncin da zai wuce abin da doka ta tanada”.

“Idan jama’a suna son arika yin tsattsauran hukunci ga masu fyade to fa dole sai sun sa ‘yan majalissarsu sunyi musu dokoki masu tsauri”.

Barrister Khalil Kabir Mantissa ya ce “siyasa tana taka rawar gani wajen hana yankewa masu aikata laifuka hukunci”.

Lauyan ya kara da cewa “‘yan sanda masu bincike suma suna taka rawar gani wajen lalata shari’a saboda rashin bin doka yayin gudanar da aikinsu”.

Lauyan ya yi kira ga iyaye da su daina boye laifin fyade idan aka yiwa ‘yarsu, saboda boyewar ce take jawo yawaitar samun masu aikata laifin.

Barrister Khalil ya jawo Hankalin iyaye akan baiwa ‘ya’yansu tarbiyyar zaman Rayuwa.

Daga karshe Matashin Lauyan ya yi kira ga Matasa Maza da Mata duk wanda lokacin yin aurensa yayi dan Allah yayi kokari yayi Aure, suma iyaye idan ‘yarsu ta girma suyi kokari su aura mata wanda take so, kada ace sai anjira yarinya ta sami saurayi mai kudi Wannan ita ce mafita.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button