Rahotanni
Talauci ne yasa Malam Ibrahim Abubakar ya rataye kan Sa a kano.
Rahotanni sun tabbatar da cewa Malam Ibrahim Abubakar (iro) dattijo Dan shekara 60 a duniya mai Sana’a a unguwar zoo-road ya rataye kan Sa ne bisa halin talauci da kuncin rayuwa dayake ciki.
A yammacin yau Alhamis dinne Malam Ibrahim Abubakar (iro) bayan yayi sallar LA asar ya idar saiga wani mai sayar da gurasa, bayan ya kirawo shi yasaya daga bisani sai yakasa cin gurasar yazauna yayi jugum, makwabtan Sa Na tambayar Sa ko lafiya kuwa, sesukaga ya tashi ya shiga shagon Sa babu bata lokaci ya rataye kan Sa Wanda sai daga baya akagano cewa Malam Ibrahim Abubakar rataye kan Sa yayi.
Makwabtan nasa sun tabbatar da cewa kuncin rayuwa da yake ciki ne yayi sanadin yankewa kan Sa wannan hukunci.
Allah yakyauta.
Daga Kabiru Ado Muhd