Tinubu ya umarci mataimakin sa daya jagoranci fito da dabarar da zata kawo tsarin rage radadi
Gwamnonin Najeriya sun goyi bayan cire tallafin man fetur ɗin da Tinubu yayi
Manyan dillalan fetur sun bada gudummawar motoci manya guda ɗari domin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur ɗin da akayi
ABUJA – Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bada umarni ga majalisar zartarwa ta kasa ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima da ƙirƙiro wani tsari na rage raɗaɗin yan Najeriya biyo bayan cire tallafin man fetur da yayi.
Umarnin na shugaban ƙasa yazo dai-dai da lokacin da gwamnonin Najeriya 36 suka goyi bayan cire tallafin na mai.
Bugu da ƙari, hakan na zuwa ne bayan manya manyan dillalan man fetur sun bada gudummawar motoci manya many guda 100 wanda darajar su takai biliyan 100 ga gwamnatin tarayya domin tabbatar da tasirin cire tallafin.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewar, gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun ne ya sanar da batun, biyo bayan jagorantar dillalan man Fetur ɗin yayin wata ziyara ga shugaban ƙasa da suka kaiwa shugaban ƙasa Tinubu, jiya a fadar mulki ta Villa dake Abuja.
Da suke zantawa da manema labarai, dillalan man fetur din sunce, sun kawo ziyarar ne domin nuna goyon baya abisa yadda shugaban ƙasar yayi ta maza wajen cire tallafin nan take.
Sai dai daga wani bangaren, mutane da yawa na tunanin ko wani irin tallafi gwamnatin zata bada? lokacin ne dai abin jira a gani.