Kasuwanci

Tallafin Kudin Da Gwamnatin Buhari Ta Ware Zata Bawa ‘Yan Najeriya Na Naira Dubu 50 Tsawon Wata Uku (Survival) Kyauta Ne Ba Bashi Ba. Naira Bliyan 75 Gwmnati Ta Warewa Tallafin, Ga Bayanin Yadda Zaku Sami Naku Da Kuma Link Din Da Zakuyi Rijista.

Spread the love

Gwamnati ta ware Biliyan 75 domin tallafawa ‘yan Najeriya, saboda jin jiki da al’umma sukayi sakamakon cutar Korona Bairos.

Yadda Ake Yin Rijista Domin Samun Tallafin…

Shin Kasan Cewa Kudin Da Gwamnati ta ware Naira Biliyan 75 na Cigaba da Rayuwa bayan Korona?

Duba Yadda Ake yin Rijistar da Kuma Abubuwan da Ake Bukata.

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta sanar da cewa an fara rajista na asusun rayuwa bayan Korona na Naira biliyan 75 don tallafawa kanana da matsakaitan masana’antu (MSMEs).

An fara rajistar tun daga ranar Litinin, 21 ga Satumba, 2020.

Babbar manufar shirin ita ce magance matsalolin tattalin arziki da kananan ‘yan kasuwa ke fuskanta a kasarnan tun bayan ballewar cutar Korona Bairos a kasarnan.

Dalili na biyu shine don taimakawa wajen bunkasa tattalin arzikin kasa ta hanyar kare ayyukan da ake da su da kuma samar da sabbin guraben aikin yi ga matasan Najeriya.

Koyaya, shirin zai fara aiki na tsawon watanni 3, wanda zai shafi kimanin ‘yan ƙasa miliyan 1.7 kuma yana da tanadi na kaso 45 cikin ɗari na mata da kuma kashi biyar na waɗanda ke da buƙatu na musamman (nakasassu).

Ofishin Bayar da Ayyuka (PDO), na shirin, ya fitar da sanarwa a ranar 20 ga Satumba a gabanin fara rajistar; Domin saukaka tsarin rajistar, an tsara yin rijistar zuwa gida uku “in ji shi.

Amma kafin mu tafi zuwa ga nau’ikan bari mu fara kawo muku abubuwan da ake buƙata da farko.

Bukatu don rajista.

  1. Dole ne a yi rajistar kamfanin a Hukumar Kula da Harkokin Kasuwanci ta Najeriya, CAC.

Amma kar a damu Idan har yanzu kasuwancin ku bai yi rijista a karkashin CAC ba, domin kuwa gwamnati ta bayar da tabbacin taimakawa ‘yan kasuwa 250,000 don yin rijista kyauta.

  1. Dole ne shugaban kamfanin ya sami lambar Tabbatar da Banki (BVN).
  2. Dole ne ya zama yana da ma’aikata wadanda basu gaza mutum 3 ba, watau kada ya kasance kai kaɗai ke yin kasuwancin.
  3. Dole ne Kamfanin ya zama mallakar ɗan Najeriya ne, kuma yaba zaune a cikin Najeriya.

Yanzu zamu koma ga nau’ikan, akwai rukuni uku da ake buƙata don wannan shirin kuma sune…

Na farko, Tallafin Kudin Rayuwa Bayan Korona, An ce an bude hanyar yin rajistar a ranar Litinin, 21 ga Satumba Satumba 2020 da karfe 10 na dare, kuma har yanzu yana gudana, kuma masu digiri sune rukuni na farko na masu cin riba da suka yi rijista.

Abu na biyu, masu neman aiki tare da Kasuwanci a cikin masana’antar baƙi za su fara rajistarsu ranar Juma’a 25 ga Satumba 2020 daga 12 A.M.

Abu na uku sauran rukunin masu neman aiki kamar; masu sana’ar hannu, masu jigilar kaya, da sauran bangarorin kananan kamfanoni zasu fara rajistar su a ranar Litinin, 28 ga Satumba, 2020, daga 12 na safe.

Rijistar ta yanar gizo ce, ga link din da zakubi kuyi rijistar👇

www.survivalfund.ng

Kuci gaba da ziyartar mu, don samun sabbin bayanai akai ko sabunta wani abu game da shirin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button