Rahotanni
Tankar Mai Ta Fadi A Hanyar Suleja Zuwa Minna A Jahar Neja.
Daga Ahmed T. Adam bagas
Wasu manyan Motoci Sunyi Hatsari Sakamakon Rashin kyan Hanya a Jahar Neja.
Motocin dai Sun hada data kamfanin A.A RANO da Kwantinar daukar kaya da Trelar daukar Kaya, Lamarin ya farune Da Yammacin Yau Laraba a Kan hanyar Suleja Zuwa Babban Birnin Jahar Neja Minna.
Hatsarin ya Auku ne a kusa da Gadar IZOM dake Karamar Hukumar Gurara ta Jahar Neja, Sai Dai Har yazuwa yanzo da Muka hada Wannan Rahoto Ba’a Samu asarar Rai ko daya Ba Sakamakon Hatsarin.
Allah ya Kiyaye Gaba.