Rahotanni

Tarar Kuɗi ₦100,000.00 ne hukuncin wanda yake a Jihar Kaduna amma bai yi Rajistar zama a jihar ba

Spread the love


Kamar yadda muka sani, Jihar Kaduna na daga Cikin manyan Jihohin Arewacin Nigeria da suke da wayewa matuƙa kuma hakan ba ya rasa nasaba da ilimin addini dana zamani da al’ummar jihar suke dashi, hakan ne yasa a ranar 1st March, 2018 Majalisar Jihar tayi wata doka mai suna “Kaduna State Residents Registration Law, 2018, (KADRR Law)” wato kundin dokar yima mazauna Jihar Kaduna Rajista, wacce ta samu sanya hannun Gwamna Nasiru Ahmad Elrufai, kamar yadda yazo a Sashi na 1, 2, dana 3 na KADRR LAW, 2018, kuma hakan ya bada damar da aka kafa Hukumar da zata kula da aiwatar da wannan tsarin kamar yadda yazo a Sashi na 4 na Kaduna State Residents Registration Law, 2018.

Amfanin yin wannan dokar tare da samar mata da ma’aikata sukutum da guda shine, don ya zama gwamnatin Jihar tana da Cikakkun bayanan duk wasu al’ummar da suke zaune a cikin jihar, ya zama tana da lissafin adadin gidajen al’ummar da suke zaune a duk faɗin jihar domin warware matsalolin tsaro, samar da walwala da Jin daɗin al’ummar, samar da ayyukan yi, inganta harkokin lafiya, samar da ilimi mai inganci, da kuma gine-ginen raya karkara da birane, da sauran su kamar yadda yazo a Sashi na 5 na KADRR LAW, 2018.

An samar da reshen wannan hukuma a duk faɗin ƙananan hukumomin dake jihar Kaduna domin saukaka ma mutane yin wannan rajistar kamar yadda Sashi na 18 na dokar ya bayyana. Sannan duk wanda yayi rajistar za’a bashi Certificate a cikin kwana 30, duba Sashi na 17 na kundin dokar.

Don haka, sashi na 16 na wannan kundin dokar ya bayyana cewa duk wani wanda yake zaune a cikin jihar Kaduna (Ko a birni ne ko a ƙauye) to dole ne yaje yayi ma gidan sa rajista da wannan hukumar, kuma zai yi haka ne a cikin wata 12 daga ranar da akayi wannan dokar, wanda kuma yake zaune a Jihar amma haya yake yi to Indai zai yi daɗewar da ya kai wata Shida a cikin jihar to dole sai yaje yayi rajistar a cikin kwana 30 kacal, koda kuwa ɗaki ɗaya ne kacal kake haya, (irin na su gwauraye) sannan idan za ka canja adireshi, ko za ka canja suna dole ne sai ka sanar ma wannan hukumar, kazalika zaka riƙa sabunta wannan rajistar ne duk bayan Shekara biyar, kamar yadda yazo a Sashi na 16 na KADRR LAW, 2018.

Duk wanda kuma ya saɓa ma wannan dokar, wato yana zaune a wani ɓangare na jihar Kaduna amma bai yi wannan rajista ba har yanzu, ko kuma a’a yazo Kaduna zai yi zaman da baiyi ƙasa da wata Shida ba amma kuma bai je yayi rajistar ba a cikin kwana 30 to ya aikata laifin da za’a ɗaure shi na tsawon Wata Shida kuma ya biya tarar Kuɗi Naira Dubu ɗari (₦100,000.00) duba Sashi na 26 na Kaduna State Residents Registration Law, 2018.

Bissalam
Shehu Rahinat NaAllah
13th April, 2023

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button