Tare da Shugaba Bola Tinubu Mun tattauna yadda farashin man fetir zai sauka Kasa ~Cewar Gwamna Uba sani.
Gwamnan jihar Kaduna Senata Malam Uba sani ne ya tabbatar da kudrin na sabuwar Gwamnati a cikin wata sanarwa bayan kammala Taron tare da Shugaban kasar Nageriya Sanata Bola Ahmad Tinubu inda gwamnan yake cewa A matsayina na Mataimakin Shugaban Kungiyar Gwamnonin Progressives (PGF) na bi sahun takwarorina, ’yan uwa masu fada-a-ji don yin wata muhimmiyar ganawa da babban jagoranmu, Bola Ahmed Tinubu a zauren majalisar zartawar fadar shugaban kasan dake Abuja.
Mun tattauna batutuwa masu mahimmanci na kasa kamar cire tallafi daga man fetur da kuma buƙatar gaggawa don ƙayyade abubuwan da suka dace don rage radadi ga ‘yan ƙasa domin gudun abinda ka iya cutarwa.
Mambobin PGF sun yi imanin cewa shugaban yana aiki bisa gaskiya domin rage radadin a wannan lokaci da ‘yan kasar ke fama da shi wanda ake sa ran gasar za ta rage farashin man fetur. Haka kuma za a tanadi isassun kayan aiki domin tunkarar kalubalen ci gaban da kasar ke fuskanta.
Daga nan ne Dandalin ya gudanar da taron sirri wanda H.E. Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo sannan ya ci gaba da wata ganawa da shugaban majalisar dattawa, H.E. Dr. Ahmad Lawan. Ganawar da shugaban majalisar ya ta’allaka ne kan bukin kaddamar da majalisar dokoki karo na 10 da za a yi nan gaba da kuma bukatar tabbatar da shugabanci na gari bisa ‘yanci.