TARIHIN DAN KASUWA ALH MUHAMMADU DANGOTE
Daga littafin Kano cibiyar Kasuwanci ta afirka wanda Marigayi Maje Ahmad Gwangwazo Allah yajiqansa ya wallafa.
Daga Sadiq Tukur Gwarzo.
Shine Muhammadu ɗangote ɗan Mallam Ali ɗan Shekarau, bafullatani mutumin kasar Kura ta jihar kano.
An haife shi a wani gari mai suna Gwate dake kasar Nijar, a sanda Mahaifansa suka je garin domin fatauci a shekarar 1903 abar tunawa, wadda turawa suka zo Kano.
Bayan haihuwar sane sai mahaifansa suka komo garinsu Kura da zama, acan ne kuma ya taso tare da samun ilimin addini. Ance Babban Malaminsa sunansa Malam Ami, makarantarsa nanan a unguwar Tukuba layin Alhaji Ibrahim Mai karofi.
Bayan da Allah yayiwa mahaifiyarsa mai suna Hadiza rasuwa, sai kakarsa mai suna Rabi ta nemi ya dawo hannunta da zama, ita kuma ta kasance tana zaune a cikin birnin kano ne. Hakan kuwa akayi, domin mahaifinsa ya aminta da haka, inda ya dawo unguwar Makafin Dala ta birnin kano da zama, anan kuma ya sauke littafin Alkurani maigirma, a hannun malaminsa mai suna Mallam Abubakar.
Daga bisani kuma sai kakar sa ta bashi jalin kuɗi Sulai biyar domin ya soma taɓa kasuwanci dasu. Ance Alhaji Muhammadu ɗangwate ya soma ne da siyar da yadiddika anan unguwar Kududdufawa, sannan ya koma cinikin kwanika a ‘yanmota ta kasuwar kantin kwari inda yakan siyi kaya daga hannun kamfanonin turawa irinsu johnholt, GBO, UAC da kamfanin PZ na kasar faransa.
Sannu a hankali sai Alhaji Muhammadu Dangwate ya shiga harkar siyasa, inda ya shiga jamiyyar N.P.C har kuma ya tsaya takarar ɗan majalisar jiha mai wakiltar karamar hukumar kura. Ance ya samu nasarar wannan zaɓe, inda suka shafe shekaru uku suna wakilci mai amfani ga alummarsu, watau daga shekarar 1963-1966.
Waɗanda suka rayu dashi, sun bayyana shi a matsayin mutum nagartacce wanda baya kin talaka, mai hakuri, mai taimakon nakasa gami da son abokai kuma.
Sannn ance yayi mu’amala da manyan mutane ta fannin siyasa da sarauta na lokacinsa.
Ance babban abin koyi a rayuwarsa shine tashi tsaye domin neman na-kai, kyauta tare da taimakon al’umma.
Shine akace akwai wata rana sanda aka haifi Marigayi General Sani Abacha, kasancewar Attajiri Alhaji Abacha amininsa ne, ya halarci wurin raɗin sunan amma a makare. To anan ne wani maroki mai suna Gizo ya bishi yana masa roko da kirari yana neman kyauta gagaruma bisa wannan baiwar haihuwa da Allah ya baiwa abokinsa. Aikuwa nan take Alhaji Dangwate yace da marokin kaje nabaka duk kayan dake jikina da kuɗaɗen aljihu na.. Wohoho.. Wannan abu ya isa makura.
A lokacin ance Fam ɗari ne a aljihunsa, gashi kuwa kusan fam ɗaya ake biyan sadakin budurwa a lokacin. Haka kuwa bayan an gama taro Alhaji ɗangwate ya cikawa wannan maroki alkwarinsa.
A fannin taimakon na kasa kuwa, ance akwai wani lokaci da Alhaji Muhammadu ɗangwate ya tura ɗansa Alhaji Garba Dangwate maiduguri fatauci.
A wannan dalili ne sai ya haɗu da Alhaji Bukar Bolori, wani ɗan kasuwa shahararre a maiduguri har kuma ya nemi yasan daga ina Alhaji Garba ɗangwate ya fito.
Daya tashi sai yake sanar masa ai sunan mahaifinsa Alhaji Muhammadu ɗangwate.. Nan take sai akaga jikin Alhaji Bukar Bolori yayi sanyi.
Daga baya sai yake sanar masa da cewa ai Alhaji Muhammadu Dangwate ne silar arzikinsa. Domin shine ke ɗora masa tallar kwanuka yana zagawa ya siyar, daga bisani yace masa ya komo garinsu zai rinka aika masa da kaya yana siyarwa.. A Haka har ya buɗe shago nasa, ya kuma zamo sahun attajiran Maiduguri.
Irin waɗannan labarai suna da yawa dangane da Marigayin.
Amma dai a karshe Allah yai masa rasuwa a shekarar 1966, ya bar ‘ya’ya 15, acikinsu harda Alhaji Aliko ɗangwate wanda yake a matsayin Attajiri na ɗaya a faɗin Afirka.
Da fatan Allah yajikansa ya kuma kyauta namu zuwan amin.