Kunne Ya Girmi Kaka

TARIHIN TSOHON BIRNIN GANGARA DA YADDA GARIN MALUMFASHI YA FITO DAGA GARESHI.

Spread the love

Daga Sadiq Tukur Gwarzo.

Kirarin Garin: Gangara Ta Naturɓe, idan kaji ina kwana bako ne.. Sai dai Nyalli Jam.

Wannan gari tsoho ne, jimawarsa kuma har takai wasu na ganin ya girmewa tsoffin birane misalin Malumfashi, Getso, Baɗari da birnin Kano.

Fulani kabilar Natirawa ne akace suka kafa garin lokaci mai tsawo daya shuɗe, sannan labari na gaskiya ya dusashe dangane da tsohon birnin, ko kuma lokacin kafuwarsa, wanda a yanzu ya zama kufai, amma dai zuwa yanzu an iya gane sashen ganuwar tsohon birnin. Haka kuma marinar garin da tsoffin kukoki nanan a inda tsohuwar rayuwar Natirawan ta auku shekaru ɗaruruwa da suka gabata.

Babban limamin Garin mai suna Mallam Adamu, ya bayyana mana cewar an samo sunan garin ‘Gangara’ ne daga kalmar ‘Gagara’, ko kuma ace garin daya Gagara acishi da yaki, domin tunda wannan birni yake babu wani sarki daya taɓa cinsa da yaki.

An samu cewa garin Gangara na usuli shahararre ne, mai zagaye da ganuwa, mai ɗauke da tarin mutane kuma. Mutane na zuwa fatauci daga sassa daban daban na kasar hausa. Har ma ance akwai zamanin da sai da gidaje suka cika birnin, har ma wasun suka rinka yin gidaje a bayan ganuwa.

Sannan kasancewar garin na fulani ne, akwai tsohuwar al’adar nan ta sharo da kuma wankan amarya da aka ruwaito tana wakana tsakankanin mazauna birnin, amma dai ance musulunci ya samu karɓuwa tun kafin zuwan Mujaddadi Usmanu ɗan fodio, don haka abubuwa irin na maguzanci basu yawaitaba.

A batun yake-yake, garin Gangara yayi zarra, tunda ance akwai wani K’aton kada mai suna ‘Nabogaji’ wanda yake cikin wani tafki dake kusa da garin, wanda kuma yake rura kuka yayin da wani bala’i ya tunkaro garin domin sanar da mazauna birnin suyi shiri.

Dukkan maruwaitan tarihin garin Gangara sun haɗu akan cewa babu wanda ya taɓa cinye garin da yaki. Wasu sunce da zarar Nabogaji yayi ruri, sai idanuwan mahara ya rufe, ya zamo basa iya ganin birnin da abinda ke cikinsa.

Yayinda wasu ke ganin tsabar jarumtar sadaukan birnin ke basu ikon mayar da keyar mahara baya.

Ance Gangara ta taɓa kaiwa garin Getso hari, taci nasara akan garin, har saida ta kori maza da mata dake garin.

Haka kuma gangara tayi yaki da garuruwan matazu, kurkujan na musawa, da malumfashi a baya-bayan nan, kuma duk ta samu nasara.

Liman Mallam Adamu ya faɗa mana cewar asalin garin malumfashi Gangara ne. Domin kuwa zamani mai tsawo daya wuce, an taɓa yin wata annoba ta ciwon ciki wadda mutanen birnin Gangara suka rinka mutuwa.

Don haka sai mutanen suka tashi izuwa gefensa suka kafa sabon gari, yayinda waɗansu suka fantsama sassan duniya.

To ance daga irin waɗannan mutanen ne wani banatire mai suna Dano (ko Dunu ) ya riski garin malumfashi a lokacin yana jeji. Sai ya sauka sannan ya sari gona domin yaɗan taɓa noma.

Da amfanin gona yazo, sai ya zamana ya samu alheri, don haka ya shiga godiya ga mai sama yana faɗin “Yanzu Na-numfasa” Daga nan kuma sai labari ya iso garinsu Gangara, inda mutane suka rinka tafiya inda yake da zummar suje suyi noma su samu riba da kuɓuta daga waccan annoba. Don haka sai suma suka rinka cewa “zamu tafi inda Dano yake Munumfasa” watau mu huta daga wannan annobar. Daga baya aka maida sunan garin ya koma ‘mulumfashi’ ko ‘Malumfashi’.

A cewar Liman, babbar hujja akan haka shine unguwar Gangarawa dake garin malumfashi. Wadda babu wata tsohuwar unguwa data girme mata.

Sunan sarautar garin Gangara shune ‘ɗan-saka’, ance ta samu ne daga wani sarkinta mai sakawa duk waɓda aka yiwa zalunci daga talakawansa. Hak kuma kasancewar sunayen tsoffin sarakunanta sun ɓata, amma dai an samu cewar a baya bayan nan sarakuna irinsu:- Dan saka Atiku, Dan saka Babba, Dan saka Nani, Dan saka Isiye, Dan saka Bello zarɓe magajin tunkuɗa, ɗan saka sarki ya-musa, ɗan saka yuguda, da ɗan saka muhammadu magajin daɗi duk sun mulketa, sai kuma dagacin dake mulkinta ayau mai suna Magaji Alh Bala ɗan muhammadi majidaɗi.

Koda yake, ance yanzu sarautar ɗansaka ta koma garin Gora bisa tashin tsohon ɗan saka Muhammadu majidaɗi daga Gangara zuwa garin na Gora saboda tsangwamar natirawa, don haka da aka turo ɗansa sai ake masa lakabi da Magaji. Saboda hak yanzu sunan sarautar garin ‘Magaji’.

Sannan kuma har gobe mutanen garin Gangara suna fahari da cewar Mujaddadi Shehu Usmanu ya sauka a garin akan hanyarsa ta zuwa Kano daga Sokoto, harma ya sahale aka soma sallar juma’a a garin, a lokacin da duk yamma da Kano daga Rimin Gado, sai malumfashi ake zuwa yin sallar jumu’a…

Zuwa yanzu dai, garin yana nan a kusa da garin Dayi, kuma yana karkashin karamar hukumar malumfashi ne ta jihar katsinan Najeriya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button