Kunne Ya Girmi Kaka

TARIHIN TSOHON BIRNIN HAUSAWA; KAFIN DABGA…

Spread the love

Daga Sadiq Tukur Gwarzo, GGA..

Daga cikin tsoffin biranen da Maguzawa suka kafa waɗanda kuma suka shahara a ƙasar Kano tun kafin zuwan jihadin Fulani akwai wannan tsohon garin mai suna ‘Kafin Dabga’.
Wani mashahurin mayaƙi bamaguje mai Suna ‘Dabga’ ne ya sari garin, shine kuma yayi masa kafi gagarumi domin kuɓuta daga dukkan harin mayaƙan wancan zamani, don haka ake kiran garin da suna Kafin Dabga.

Garin ya haɓaka, ya shahara, kuma ya samu ɗaukaka. A baya ance zagaye yake da ganuwa, wadda aka yiwa ƙofofi guda huɗu. A kowacce kofa mace da namiji ne suka tsaya aka yaɓe su da ransu saboda surkulle, sannan da wata ƙaya sarƙaƙiya ake rufe kofar shiga birnin ba da ƙofa ba. Don hakangarin ya kasanxe mai tsananin uytsaro.

Idan yaƙi yazo, daka ake sanyawa ayi da dare, sai mayaƙa su shirya da hanzari. Masu kwari da baka su hau saman ganuwa, masu masu da takubba su shige surƙuƙi suna sauraron ko-ta-kwana.

Daga cikin sarakunan da ake iya tuna sunayen su a wannan gari, ance sunan Sarkin Kafin Dabga na farko Dugaji, Bamaguje ne, yayi wannan sarauta kimanin shekaru 400 da suka gabata, ko da yake tsufan kukokin garin da marinar garin na iya kaiwa sama da waɗannan shekarun.

Amma dai kwatancin shekarun da ake tsammanin an soma sarauta a garin kenan.
Bayan mutuwar sa sai shi Dabga yayi mulki, wanda asali ance ya zamo tamkar uba ne mai ɗora wanda yake so shugabanci a garin.
Daga shi sai Also, sannan sai Abdullahi ya fara mulki a zamanin da Fulani suka karɓe sarauta.

Akwai manyan gidajen da har yanzu ake ambata a garin, waɗanda sukayi gadon shugabancin garin, da kuma jarumta tun kafin jihadin fulani, misalin su shine; Gidan Nazundumi, Gidan Dankali, Gidan Butsatsa, da Gidan Gigo.

KUKAR ƳAR FULANI
Akwai wata kuka mai tarihi a wannan gari mai suna kukar ƴarfulani. Ita ƴar fulanin aljanna ce wadda ake da yaƙinin akan wannan kuka gidan ta yake.

Ance a zamanin baya, tana taimakon garin lokacin da yaƙi ya taso, ko kuma wani mugun abu ya nufo garin, inda take sanya sarƙa ta kanan-naɗe mahara.
Ance kuma a zamanin mulkin sarki Abdullahi na garin, yana sanyawa a kai mata ƙwaryar nono da farin goro duk ranar juma’a, ita kuma takan yin shewa da godiya yadda duk wanda ke garin sai ya ji.

TARWATSEWAR KAFIN DABGA..
Kafin garin kafin Dabga ya samu raguwar mazauna, ya kasance shahararre mai cike da mutane wanda ya kasance daga gari-gari akan zo masa don yin fatauci.

Sannan garin yayi yaƙe-yaƙe da biranen dake kusanci da ma na nesa misalin Gammo da Ƙiru, har ma ana cewa ba a taɓa cin garin da yaƙi ba.

Sai dai wata annoba da ta faɗawa garin ce tayi sanadiyyar ɗaiɗaicewar sa.

Ance wata baƙar aljana ce ta rinƙa halaka mutane.

Idan dare yayi sai tayi shewa, tace ‘Kun Taru?’, to fa duk wanda yayi ko da gyaran murya a wannan daren ba zai wayi gari ba. Daga nan aka sanyawa annobar suna ‘Kun-Taru’.

Don haka aka rinƙa wayar gari da gawarwakin mutane burjik waɗanda ta halaka, hakan yasa mutanen garin da dama suka ƙaurace masa.

A yanzu dai, garin Kafin Dabga yana nan ƙarƙashin garin Karaye, a jihar kano.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button