Tashin Hankali: Karanta Yadda Matan Aure Sama Da 30 Suka Haihu A San-sanin ‘Yan Gudun Hijira A Katsina.
A kalla Matan Aure 30 ne Suka Haihu a Sansanin su Na Gudun Hijira a Katsina.
A kalla matan Aure Talatin ne suka haihu a Sansanin yan gudun Hijira a Jahar Katsina.
Wannan Al-amari ya farune Sakamakon Matsalar tsaro da ke addabar Jahar, Hakan ya tilastawa Mazauna Kauyuka da dama Barin Garuruwansu Suna Zaman Hijira a wasu Manyan Garuwan Jahar.
Matsalar tsaron wanda ya sanya a Kwanakin baya matasa suka Yi zanga zangar Lumana domin Jawo hankalin mahukunta su Fuskanci Halinda suke Ciki, Tuni dai Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya Tura Wakilansa Jahar Domin Tattaunawa da Gwamnan Jahar Aminu Bello Masari domin Kawo karshen Kashe kashe da akewa Al’ummar Jahar.
Masu karatu Wacce Hanya za’abi domin kare Martabar Mata Masu Juna biyu a Sansanin Gudun Hijira…???
Ahmed T. Adam Bagas