Tattaunawa da ‘yan ta’adda ba shine Mafita ba ga Nageriya ~Inji Abdulsamu Abubakar
Janar Abdulasalmi Abubakar (mai ritaya) ya ce tattaunawa da ‘yan fashi ba shi ne mafi kyawun hanyar dakatar da yin fashi ba.
Da yake magana lokacin da tawagar kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) suka ziyarce shi a gidansa da ke Minna, Jihar Neja, tsohon shugaban ya ce mai yiwuwa ne a tilasta wa gwamnati ta amince da tattaunawa kan sakin dalibai wadanda aka sace a Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati dake Kagara.
Ya roki gwamnati da ta yi la’akari da duk hanyoyin da za a bi don ganin an sako daliban.
“Tattaunawa ba ita ce hanya mafi kyau ba amma babu mafita ‘Ya’yanmu sun sace sama da kwana biyar, koda kuwa kun san inda suke, zai zama wauta idan aka tunkaresu da fada domin akwai yiwuwar a samu asarar rayuka.
“Wani lokaci ana bukatar ganin hanya mafi kyau da za ku iya magana da wadannan mutane marasa zuciya don ganin yadda za ku saki mutanen nan. Amma tattaunawa ba ita ce hanya mafi kyau ba.
“Ya kamata hukumomin karfafa doka su hada kai don tsara sabbin dabaru kan yadda za a shawo kan matsalar,” in ji shi.
Gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti, wanda shine Shugaban taron, shi ne ya jagoranci tawagar zuwa gidan tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Ibrahim Babangida, wanda ya yi magana kan halin da wadanda aka sace din na Kagara suka shiga.
“Tsaron yaran yana da mahimmancin gaske a yanzu. Muna so su fito lafiya ba tare da wani ya ji ciwo ba. Duk wani matakin da gwamnati za ta dauka don ganin an sake su zai yi daidai, ”inji shi.
Wadanda abin ya shafa sun kwashe mako guda a hannun masu garkuwar.