TAURARIN FINA-FINAN HAUSA…..
Shiri Na Biyu……
Mai karatu barka da warhaka, da fatan kana cikin koshin lafiya.
Acikin shirin namu na yau, zakuji Amsar tambayar
@Zulyadaini Haruna.
@Mamuda Isah Bichi.
@Fatima Isah Jos.
@Safiya Musa Zaria.
@Salmanu Sani Daga Yobe.
@Fauziyya Saminu Daga Abuja.
Wadanda suke son Jin tarihin Shahararren Jarumin Kannywood dinnan, Wato SANI MUSA DANJA.
Jaridar Mikiya ta samu damar tattaunawa dashi…..
Ga dai yadda tattaunawarsu da wakilin Mikiya…..
Mikiya: Wanene Sani Musa Danja?
Danja: To Ni dai sunana Sani Musa Danja, An haife Ni a ranar 20 ga watan Afrilu, shekara ta 1973 a karamar hukumar
Fagge dake Kanon Nijeriya, a gidan Mahaifina Alhaji Musa Abdullahi da kuma Mahaifiyata Hajiya Risikat. Nine babba a cikin ’ya’ya bakwai
da iyayena suka haifa.
Na halarci makarantar firamare ta ‘Yan Sanda daga shekarar 1979 zuwa 1980, Sannan nacigaba da makarantar sakandare ta Government Junior Secondary School Kawaji, a shekara ta 1985 zuwa 1989, Na tafi
Kwalejin Rumfa don kammala karatuna na sakandare a shekarar 1989 zuwa 1991. Sannan nacigaba da karatuna na gaba da secondire zuwa FCE Kano inda na samu nasarar samun takardar shaidar NCE.
Mikiya: Ina ka samo lakabin Danja?
Danja:: Sunane Wanda na samoshi tun Ina karami, Saboda taurin kaina da kuma dagewa akan duk abunda na tasa.
Mikiya:: Yaushe ka tsinci kanka a harkar fim?
Danja:: Na fara shiga masana’antar shirya fina-finan Hausa wato Kannywood a shekarar 1999, tare da fim dina mai suna DALIBAI, fim ne wanda na kirkira, kuma na nuna shi tare da abokin aikina wato Yakubu Muhammad.
Alhaji Rabi’u Kofar Wambai shine ya kira ni, yace dani “Ya kamata ace ka shiga harkar fim, Saboda irin yadda naga ka iya rawa, kuma kana da kyakkyawar mu’amala da mutane, hakan kuwa akayi Inda na fara da fim din DALIBAI. Bayan nasarar da Na samu ta fim din (Dalibai), sai kuma na kara fitowa a wani fim mai suna ADON KISHIYA a shekara ta 2000, sannan sai wani fim kuma mai suna KWARYA TABI KWARYA, Wanda shine babban fim ɗin da nayi tare da jaruma Jamila Haruna a shekara ta 2000. Daga nan kuma aka cigaba dayi har zuwa lokacin da muke a yanzu.
Mikiya: Daga wane lokaci ne tauraruwarka ta fara haskawa?
Danja:: Gaskiya Ni na fara samun daukaka tun daga lokacin da fuskata ta fara bayyana a fim.
Mikiya::Shin Wai ‘Yan Fim masu bata tarbiyya ne?
Danja:: A’a ‘Yan fim masu fadakarwa ne, sai dai ba za’a rasa na banza acikinsu ba, domin duk Inda al’umma ta taru, sai ka samu akwai na kirki dana banza a gurin, to haka abun yake a masana’antar kannywood.
Mikiya::Wacce Tambaya ce ka gaji da amsawa?
Danja:: Sani Musa Danja “Wai dagaske baku shiri da Ali Nuhu, wannan itace tambayar dana gaji da amsawa.
Mikiya::Wacce amsa kake basu??
Danja:: Nakan ce musu a’a wannan maganar ba gaskiya bace, akwai kyawawan alaka tsakanina da Ali Nuhu.
Mikiya::Matan ka nawa?
Danja:: Matata guda daya ce rak, wato rabin raina, abun sona kuma abun alfaharina Hajiya Mansurah Isah.
Mikiya:: Yaranka nawa?
Danja::: Yarana guda hudu ne.
Mikiya::Shin zaka kara aure?
Danja:: Hmmmm Nima bansani ba.
Mikiya:Shin ka taba samun aikin jakadanci?
Danja:: Eh Nayi aikin jakadanci a Kamfanin Global Health Forom, Starcoms, M.T.N, GLO da Sauransu.
Mikiya::Shin kana da kamfanin shirya Fina-Finai?
Danja:: Eh Ni keda rabin hannan jarin Kamfanin 2Effect Emfire.
Mikiya:: Akalla Fina-Finan ka zasu Kai nawa?
Danja:: Akalla na shirya Fina-Finai guda 350.
Mikiya:: Wanene babban abokinka a masana’antar kannywood?
Danja:: Shine Yakubu Muhammad.
Mikiya:: Dagaske Wai kafi kowa kudi a masana’antar kannywood?
Danja::: hhhhhhhhhhh Gaskiya Nima bansani ba.
Mikiya:: Ka taba samun kambun girmamawa?
Danja:: Gaskiya na samu kambun girmamawa marasa adadi, wasu na samesu a Nigeria, wasu Kuma a kasashen ketare.
Mikiya:: Wane fim naka kafi so?
Danja:: Wadanda ‘yan kallo suka fi so.
Mikiya:: Me yafi burgeka idan ka fito cikin al’umma?
Danja:: Irin yadda mutane suke nuna min so da kauna, da kuma irin yadda mutane suke min kyaututtuka.
Mikiya:: Alh.Sani Musa Danja, a matsayinka na Jarumi, Wacce shawara zaka bawa masu son shigowa harkar fim, har suma suga sun zamo kamar Sani Danja?
Danja:: Shawarar itace, su zamo masu biyayya ga manyansu, Sannan su zamo masu hakuri da juriya, Sannan su zamo masu Ilimin addini dana zamani, domin har ga Allah yanzun harkar fim ta chanza, dole sai mutum ya kasance mai Ilimi.
Mikiya::Alh.Sani Musa Danja muna Godiya bisa lokacin da aka bamu.
Danja:: Hmmmm Nima Na Gode Sosai. Ina addu’ar Allah ya karawa Kamfanin Jaridar Mikiya Mahanga Labarai Albarka, Sannan Kuma Allah ya kara daukaka ma’aaikatan ta.
Wannan itace karshen tattaunawar mu da Sani Musa Danja.
Kuma zaku iya aiko da sakonnin tambayoyin ku, ta Numbar Whatsapp namu kamar haka 08138968615. A madadin Shugaban shirin M.Inuwa MH. Sai Wanda ya tsara Shirin Sabiu Danmudi Alkanawi, Ni dana gabatar muku da shirin SUNUSI (D) DANMALIKI, Nake cewa sai mun hadu a wani satin….